logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira ga kasa da kasa da su ci gaba da nuna goyon baya ga Somaliya

2024-02-20 15:16:35 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da jawabi  yayin taron kwamitin sulhu game da batun Somaliya, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su ci gaba da nuna goyon baya ga Somaliya.

Zhang Jun ya bayyana cewa, bana shekara ce mai muhimmanci ga Somaliya kan ci gaban siyasa da tabbatar da tsaro da kuma sake gina kasar. Da farko, ya kamata a nuna goyon baya ga Somaliya wajen kiyaye kwanciyar hankali na siyasa. Na biyu, ya kamata a nuna goyon baya ga Somaliya wajen tabbatar da tsaro. Na uku, ya kamata a nuna goyon baya ga sake gina zamantakewar tattalin arziki ta Somaliya. Bangaren Sin yana maraba da gwamnatin tarayyar Somaliya ta kaddamar da shirin “Hangen Karni na 2060” da kuma tsara ayyuka masu muhimmanci na ci gaban kasar. (Safiyah Ma)