logo

HAUSA

Sin za ta yi aiki tare da Spaniya wajen inganta tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin kasashe

2024-02-20 14:04:56 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Spaniya wajen inganta yin shawarwari da hadin gwiwa a tsakanin dukkan kasashen duniya, da yin watsi da bambance-bambance, da gina al’umma mai makomar bai daya ga bil’Adama, don magance kalubalen da duniya ke fuskanta.

Wang, wanda kuma mamban ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da sarkin Spaniya Felipe VI.

A nasa bangare Sarki Felipe VI ya bayyana cewa, a cikin shekaru 50 da suka gabata, kasashen Spaniya da Sin sun samu bunkasuwa cikin sauri, kuma sun samu ci gaba cikin lumana ta hanyar yin hadin gwiwa a aikace, da yin cudanya da juna. Kasar Spaniya za ta kara fadada hadin gwiwa da Sin a sabbin bangarorin.

Wang ya kara da cewa, ci gaban da jama'ar kasar Sin fiye da biliyan 1.4 suka samu ta hanyar zamanantarwa, babban ci gaba ne ga wayewar kan dan Adam, kuma zai samar da muhimman damammaki ga duniya, yana mai cewa, tarihi ya tabbatar, kuma zai ci gaba da tabbatar da cewa, bunkasuwar kasar Sin tana kara karfafa zaman lafiya da daidato a duniya. (Yahaya)