logo

HAUSA

AU ta kaddamar da shirin shekaru goma na biyu na ajandar 2063

2024-02-20 10:08:02 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Afirka AU ta kaddamar da shirin shekaru 10 na biyu na ajandar raya Afirka nan da shekarar 2063, inda ta zayyana muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar, da kuma manufofin da za a cimma a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Shirin wanda aka fi sani da shekaru goma na kara habaka wanda zai gudana daga shekarar 2024 zuwa 2033, an amince da shi ne a zaman taron shugabannin kasashen kungiyar karo na 37 da ya gudana daga ranar 17 zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu a hedkwatar AU da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Kungiyar ta AU ta bayyana kaddamar da aiwatar da shirin ci gaban nahiyar na shekaru goma na biyu, da kuma abubuwan da suka sa a gaba a matsayin wani muhimmin ci gaba mai cike da tarihi ga kungiyar tarayyar Afirka, da mambobinta, da ma daukacin 'yan Afirka.

Ta ce, "Shirin aiwatar da ajandar ci gaba na shekaru 10 na biyu na shekarar 2063, wata taswira ce mai karfin gaske kuma mai cike da buri na sauye-sauyen Afirka. Wannan wata alama ce ta jajircewa da kudurin al'ummar Afirka wajen tsara makomarsu." (Yahaya)