logo

HAUSA

Shugaban Guinea ya rushe gwamnatin kasar

2024-02-20 09:54:36 CMG Hausa

Shugaban rikon kwarya na kasar Guinea Janar Mamady Doumbouya, ya rushe gwamnatin kasar dake karkashin firaminista Bernard Goumou a jiya Litinin.

Bisa umarnin shugaban wanda minista sakatare janar mai kula da fadar shugaban kasa Amara Camara ya karanta ta kafar talabijin, manyan sakatarori da mataimakansu da shugabannin ma’aikatu, su ne za su ci gaba da kula da harkokin kasar kafin kafa sabuwar gwamnati.

Umarnin dai bai bayyana dalilin rushe gwamnatin ba. (Fa’iza Mustapha)