Kungiyar Houthi ta sanar da kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka biyu
2024-02-20 10:44:45 CMG Hausa
Kungiyar Houthi dake Yemen, ta sanar da kai hare-haren makamai masu linzami kan jiragen ruwa biyu mallakar Amurka a gabar tekun Aden, tana mai ikirarin samun nasara.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta gabatar ta tasharta ta tauraron dan Adam mai suna al-Masirah, kakakin kungiyar Yahya Sarea, ya ce hare-hare kan jiragen ruwan Amurka da ake wa lakabi da Sea Champion da Navis Fortuna, sun isa inda aka yi niyya, amma bai bayyana asarar da suka haifar ba.
A cewarsa, adadin hare-haren da Houthi ta kai cikin sa’o’i 24 sun kai 4. Da farko, kungiyar ta kai hari ne kan jirgin ruwan Birtaniya, lamarin da ya yi sanadin nutsewarsa baki daya. Sannan ta harbo jirgi mara matuki na MQ9 na Amurka daga sararin samaniyar yankin Hodeidah, yayin da ta kai hare-hare biyu na karshe kan jiragen ruwan Amurka 2.
Cikin sanarwar, kakakin ya ce hare-haren kungiyar Houthi a tekun Bahar Maliya da tekun Arabiya za su karu kuma ba za su tsaya ba har sai Isra’ila ta dakatar da farmakinta kan kungiyar Hamas da janye kawanyar da ta yi wa Falasdinawa a zirin Gaza. (Fa’iza Mustapha)