logo

HAUSA

Babu wata kasa da za ta tsira muddin akasarin kasashen duniya na cikin tashin hankali

2024-02-20 17:19:30 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira da a yi kokarin kaucewa ra’ayin tafka asara, yayin da yake karin haske kan rahoton shekara-shekara da aka fitar gabanin kammala taron tsaro na Munich, wanda ya bayyana damuwa kan karuwar ra’ayin tabka asara.

A yayin da ake fuskantar karuwar tabarbarewar al’amuran duniya da suka haifar da kuncin rayuwa ga tarin al’ummomi, har yanzu wasu kasashe sun fi mayar da hankali kan rungumar ra’ayin cin riba daga faduwar wata kasa. Abun da har yanzu wasu kasashe suka gaza fahimta shi ne, babu wata kasa da za ta samu kwanciyar hankali muddun akasarin kasashen duniya na fama da tashin hankali ko rashin tsaro ko talauci.

Abun kunya ne da takaici, a ce manyan kasashe sun zama masu cin riba daga asarar kananan kasashe maimakon zama abun dogaro ko wadanda ke tallafawa domin ganin ci gaban kasashen dake musu kallon ababen koyi.

Kamar yadda Wang Yi ya bayyana, bangaren kasar Sin ya yi imanin cewa, ra'ayin cin moriya da faduwar wani, da neman mayar da wasu saniyar ware, da yunkurin yin fito-na-fito na wani gungu, su ne ke haifar da ra’ayin "tabka hasara".

To ina mafita?

Kamar dai yadda kullum kasar Sin ke kira, mafitar ita ce tabbatar da daidaito tsakanin kasa da kasa ta hanyar inganta hulda da cudanya a tsakaninsu bisa gaskiya da adalci. Idan dai za a kyautata hulda bisa gaskiya da sanin ya kamata, to tabbas babu wani bangare da zai so ganin faduwar abokan huldarsa. Ya kamata a hada karfi da karfe don a gudu tare a tsira tare.

Yanayin da duniya ta shiga, ko in ce wasu tsirarun kasashe suka jefa duniya ciki, ta shaida cewa, idan har ba a dawo kan turbar da ta dace ta daidaito da adalci ba, to ba za a samu kyakkyawar makomar da ake buri ba.

Kasar Sin mai rajin ganin an samu ci gaba da tabbatuwar adalci da cudanya da hadin gwiwar bangarori daban daban, ita kadai ba za ta iya tabbatar da hakan ba. Dole manyan kasashe su mara mata baya, su ba da gudunmawarsu bil hakki da gaskiya, su ajiye girman kai da hadama, a hada hannu a ceto duniya daga durkushewa. (Fa’iza Mustapha)