logo

HAUSA

Wang Yi: Samun Nasara Tare Ita Ce Makomar Siyasa

2024-02-19 21:06:16 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira da a yi kokarin kauce wa ra’ayin "tabka hasara", yayin da yake karin haske kan rahoton tsaro na Munich na shekarar 2024.

Wang ya ce, ra’ayin da wasu ke da shi na "tabka hasara", ba zabi ne da hankali zai dauka ba, kuma cin nasara tare shi ne makomar dan Adam.

Rahoton na shekara-shekara da aka fitar a Litinin din nan gabanin kammala taron tsaro na Munich, ya jaddada damuwar da ake da ita kan ra’ayin "tabka hasara", yayin da ake samun karuwar tashe-tashen hankula a fannin siyasa da karuwar rashin tabbas na tattalin arziki.

A cewar rahoton, gwamnatoci da dama ba sa mai da hankali kan cikakkiyar fa'idar hadin gwiwar duniya, maimakon haka suna kara nuna damuwa cewa, suna samun moriya kasa da ta saura.

Wang ya ce, rahoton ya nuna yadda nahiyar Turai ke tunani da kuma damuwar da duniya ke ciki.

Ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya yi imanin cewa, ra'ayin cin moriya da faduwar wani, da neman bayar da wasu saniyar ware, da yunkurin yin fito-na-fito na wani gungu ne ke haifar da ra’ayin "tabka hasara". Yana mai cewa, kasashe da yawa sun fahimci cewa, tilas ne a kaucewa hasara.

Ya kara da cewa, ya kamata mu yi aiki tare, mu yi la’akari da muradun wasu tare da kare muradun kanmu, da inganta ci gaban hadin gwiwa tare da neman ci gaban kanmu, ta yadda za mu samu nasara tare, kuma nasara shi ne burin da ya kamata mu bi tare.

Wang ya ce, idan har ana son cimma nasara tare, kamata ya yi kasashe su zabi hadin kai kan rarrabuwar kawuna, hadin gwiwa kan sabani da bude kofa ga juna. (Ibrahim)