logo

HAUSA

Kasar Sin Karfi Ce Ta Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya

2024-02-19 15:43:25 CMG Hausa

A duniyarmu ta yau, kasar Sin ta kasance amintacciyar kasa, mai daukar nauyi da dawainiyar tsarin harkokin duniya dake cike da rashin kwanciyar hankali da daidaito, da bude kofa ga dukkan nau'o'in hadin gwiwar bangarori daban-daban. Yayin da kasashen yammacin duniya ke kokarin raba gari da kasar Sin, da ma kokarin kawo tsaiko ga ci gabanta da dunkulewar duniya baki daya, yanzu kasar Sin ce ke kokarin kira da tabbatar da daidaito tsakanin bangarori daban-daban da inganta tsarin duniya.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken "Taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya mai cike da tashin hankali" a taron tsaro na Munich da aka gudanar a ranar 17 ga watan Fabrairu.

Taron Tsaro na Munich (MSC) taro ne na shekara-shekara kan manufofin tsaro na kasa da kasa a birnin Munich na Jamus. Asalin taken ita ce: "Zaman lafiya ta hanyar tattaunawa", kuma taron na wannan shekara ya maida hankali kan ko kasashen duniya sun shirya samar da zaman lafiya a aikace ko za su ci gaba da maganar baka ne kawai?

Kasar Sin mai fada da cikawa, ta ba da gudummawar rundunar wanzar da zaman lafiya mafi girma duniya kuma kasa ta biyu da ta fi ba da gudummawar kasafin kudin Majalisar Dinkin Duniya. Ta yi alkawarin cika alkawuran COP28, da tafiyar da harkokin kirkirarriyar basira wato AI na duniya, da kuma zama jigon habaka harkokin duniya. Kasar Sin ta yi kira da a tsagaita bude wuta a Ukraine da Falasdinu. Wannan karin sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya da ya rataya a wuyan kasashen duniya yana tafiya kafada da kafada da karfin kasar Sin da tasirinta a cikin al'ummar duniya, bisa ci gaban tattalin arzikinta.

Tabbatar da tsaro a duniya ga kowa da kowa yana nufin kwarewa wajen "aiki da cikawa". Hakan zai faru ne a lokacin da kasashen duniya suka hade waje guda domin tabbatar da tsaro na gama gari, ba wai a bar wata kasa da aikin tabbatar da tsaron duniya yayin da wasu kasashen ke mata zagon kasa ba. Kudaden da aka kashe kan aikin soji a duniya ya karu zuwa dala biliyan 2240 a shekarar 2022 kuma yana ci gaba da haurawa kawo yanzu, kamar yadda lamarin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a duniya. Saboda ba a kasashe wadannan kudaden ta hanyoyin da suka dace ba, shi ya sa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. An kashe kudaden ne bisa son ran kasashen yamma cike da rashin amana game da hakikanin manufarsu da muradunsu, hakan ya sanya ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi, bai kammala jawabinsa ba sai da ya jaddada tafiyar da harkokin diflomasiya bisa amana.

Don haka, a mahangar kasar Sin, hanyar da ta dace ga amincewa da juna ita ce hanyar bayyana irin gudummawar da Sin ke bi wajen daidaita harkokin duniya, da bukatunta, da kiyaye jajayen layuka masu nasaba da tashin hankali. (Muhammed Yahaya)