logo

HAUSA

Jirgin C919 na Sin ya halarci bitar bikin nune-nune jiragen sama na Singapore

2024-02-19 10:02:51 CMG Hausa

Jirgin fasinja samfurin C919 na kasar Sin, ya yi gwajin tashi jiya Lahadi a Singapore, a wani bangare na shiryawa bikin nune-nunen jiragen sama dake karatowa.

Yayin bikin nune-nunen jiragen sama na Singapore na shekarar 2024, za a gabatarwa jama’a jirage 5 da kamfanin kera jiragen saman fasinja na kasar Sin ya samar, ciki har da C919. Bikin zai gudana ne daga ranar 20 zuwa 25 ga watan nan na Fabreru.

Bikin zai samu halartar kamfanoni sama da 1,000, kuma ana sa ran zai ja hankalin ‘yan kasuwa mahalarta 50,000 daga kasashe da yankuna sama da 50.

Mashirya bikin sun bayyana cewa, a karon farko za a kafa rumfa ga kamfanonin jiragen sama na kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)