logo

HAUSA

Isra’ila ta ce ba ta amince da a kafa kasar Falasdinu ba

2024-02-19 14:05:07 CMG Hausa

A cikin wata sanarwa da ofishin firaministan Isra’ila ya fitar a ranar 18 ga wata, ya ce Isra’ila ta yi watsi da “umarnin kasa da kasa” kan batun warware rikicin Isra’ila da Falasdinu, kuma tana ci gaba da nuna adawa da amincewa da Falasdinu a matsayin kasa. 

Sanarwar ta ce, za a iya cimma mafita kan batun Isra’ila da Falasdinu ne ta hanyar yin shawarwari kai tsaye tsakanin bangarorin biyu ba tare da wani sharadi ba. (Muhammed Yahaya)