Rikicin kabilanci a Papua New Guinea ya haddasa mutuwar mutane 64
2024-02-19 20:54:18 CMG Hausa
Kafofin watsa labarai na kasashen Papua New Guinea da Australiya sun ba da labari yau Litinin 19 ga wata, cewar mutane a kalla 64 sun mutu sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a lardin Enga na kasar Papua New Guinea a kwanan nan.
Rikicin ya barke ne da sanyin safiyar jiya, inda 'yan sanda suka gano gawawwaki 64. Har yanzu dai ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka mutu, da alamun yawan wadanda suka mutu zai iya karuwa.
A cewar kafar yada labarai ta Australiya, an harbe mutanen ne a wani kwanton bauna. Rikicin da ya taba barkewa tsakanin wadannan kabilu a shekarar da ta gabata, ya haddasa mutuwar mutane fiye da 60.
Rahotanni na cewa, rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin kabilu daban daban a lardin Enga na kara tsananta a ‘yan shekarun da suka gabata, wadanda ke shafar kabilu 17. (Hamza Wang)