logo

HAUSA

Ministan Tsaron Jama’ar Kasar Sin Ya Gana Da Sakataren Tsaron Cikin Gida Na Amurka

2024-02-19 19:47:09 CMG Hausa

A jiya ne, dan majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan tsaron jama’a na kasar Wang Xiaohong ya gana da sakataren tsaron cikin gida na kasar Amurka Alejandro Mayorkas a birnin Vienna na kasar Austria.

Wang ya bukaci bangaren Amurka da ya dakatar da nuna tsangwama da yi wa daliban kasar Sin tambayoyi ba tare da wani dalili ba, da kuma tabbatar da ganin jama’ar Sin sun sami damar shiga Amurka cikin adalci da mutunci. Ya kuma bukaci Amurka ta aiwatar da matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron ofisoshin jakadancin Sin da ma’aikatansu dake Amurka. Wang ya bukaci Amurka da ta daina sanya takaitawa kan bayar da takardun Visa ga hukumomi da ma’aikatan Sin masu ruwa da tsaki, da gyara kuskurenta na sanya kasar Sin a cikin jerin “manyan kasashen dake samar da miyagun kwayoyi”.

Bangarorin biyu sun amince da aiwatar da muhimmin ra’ayi da shugabannin kasashensu suka cimma, da ci gaba da yin shawarwari da hadin gwiwa a fannonin yaki da miyagun kwayoyi da aiwatar da doka, da kulawa da muradun juna, da warware matsaloli yadda ya kamata, bisa tushen mutunta juna, da daidaita bambance-bambance da yin hadin gwiwar samun moriyar juna, a kokarin ba da gudummawa ga ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ba tare da wata matsala ba. (Hamza Wang)