logo

HAUSA

Wang Yi ya yi tir da karairayin da ake yi game da Xinjiang a Munich

2024-02-19 10:43:51 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi tir da karairayin da ake yadawa game da kisan kiyashi da kuma tilastawa mutane yin aiki a jihar Xinjiang yayin da yake amsa tambayoyi a taron tsaro na Munich a ranar Asabar.

Ya ce, tun lokacin da aka kafa yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa, yawan mutanen Uygur ya karu daga miliyan 3 zuwa sama da miliyan 12 ya zuwa yanzu. Kuma ana ba da kariya ga ‘yancin gudanar da addini na dukkan kabilu da ke wurin, inda ya ba da misali da cewa musulmai na da isasshen wuraren ibada kuma gwamnati ta dauki nauyin gyara da kula da masallatai.

Da yake magana game da zargin da ake yi cewa ana tilastawa mutane yin aiki, Wang ya ce, yin amfani da wannan zargi a matsayin uzuri don shafawa kasar Sin bakin fenti, wata manufa ce ta kwace wa al’ummar Uygur ayyukan yi tare da hana su sayar da hajojinsu.

Ya kara da cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu cikin sauri ya haifar da rashin jin dadi da damuwa a tsakanin mahukuntan wasu kasashe, shi ya sa suke yada karairayi game da jihar Xinjiang don haifar da cikas, ta yadda za a hana ci gaban kasar Sin da farfado da tattalin arzikinta.

A ranar 18 ga watan Fabrairu ne aka kammala taron kwanaki uku na taron tsaro na Munich karo na 60 a birnin Munich na kasar Jamus. A yayin taron, mahalarta daga kasashe daban-daban sun tattauna batutuwa kamar rikicin Ukraine, rikicin Isra'ila da Falasdinu da kuma tsarin kasa da kasa. (Yahaya)