logo

HAUSA

Gwamnan jihar Borno: jihar na fuskantar matsalar tashe-tashen bama-bamai da aka bibbinne a wasu manyan titunan jihar

2024-02-19 08:50:56 CMG Hausa

Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci al’ummar jihar da su himmatu wajen gudanar da addu’o’i domin samun saukin matsalolin tsaro da kuma na karuwar farashin kayayyakin abinci a kasa baki daya.

Ya bukaci hakan ne lokacin ya gudanar da wata ganawa ta musamman da ’yan kasuwa da shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a gidan gwamnatin jihar, ya ce halin da ake ciki yanzu a jihar yana bukatar addu’a sosai. 

Wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun karuwar matsalolin tashe-tashen bama-bamai da ake binnewa a gefen wasu daga cikin manyan tituna da kuma gonakin dake jihar ta Borno.

Ya ce, wannan mummunan halayya ta dasa boma-bamai ba wai kawai yana barazana ne ga ’yan kasa ba kadai, yana kawo cikas ga safarar kayayyakin amfanin yau da kullum wadanda za su kawo ci gaban jihar.

Gwamnan na jihar Borno ya ce, gwamnati na kokarin wajen bunkasa sha’anin noma ta hanyar samar da kayayyakin aikin gona da takin zamani da sauran agaji ga manoma duk dai domin a saukakawa al’umma matsalar tsadar kayan abinci. 

Gwamnan ya kuma kara kira ga al’ummar jihar ta Borno cewa, “Ina kira ga al’umma da su gudanar da azumin yini daya ranar Litinin din nan 19 ga watan Fabarailun 2024, ina kira a gare mu da mu gudanar da addu’o’in zaman lafiya da wadata domin ci gaban wannan jiha tamu da ma kasa baki daya.”

Daga bisani gwamnan na jihar Borno ya bukaci ’yan kasuwa da su rinka rangwame a kan kayayyakinsu a matsayin tasu gudummawa wajen fitar da al’umma daga mawuyacin hali da ake ciki yanzu haka. (Garba Abdullahi Bagwai)