Kasar Sin ta ci nasarar harba da kuma dawowar wata roka samfurin Kuaizhou
2024-02-19 08:50:29 CMG Hausa
A karshen watan jiya, wani kamfanin nazarin roka na kasar Sin ya ci nasarar harba da kuma dawowar wata roka samfurin Kuaizhou wadda ake iya sake amfani da ita sau da yawa. Wannan nasara ta alamta cewa, kamfanin ya riga ya mallaki fasahar harba da kuma dawowar rokar da ake iya amfani da ita sau da yawa. (Sanusi Chen)