logo

HAUSA

Kamfanonin wutar lantarki na gamayyar kasashen yankin Sahel AES za su taro a birnin Ouagadougou

2024-02-19 09:28:07 CMG Hausa

Kasar Burkina Faso za ta karbi bakuncin taron shawarwari na kamfanonin wutar lantarki na gamayyar kasashen yankin Sahel AES da suka hada Nijar, Mali da Burkina Faso da zai gudana daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Fabrairun shekarar 2024 a birnin Ouagadougou.

Daga birnin Yamai, Mamane Ada ya turo mana da wannan rahoto. 

Kasar Burkina Faso ta zama kasa ta farko da taron ministocin makamashi da takwarorinta suka karrama domin shirya babban taron fasalta makomar makamashi da dorewarsa a wannan sabuwar kungiyar ta yankin Sahel.

Taron zai gudana bisa taken “wadanne dubaru domin tsaron samar da wutar lantarki ga kasashen kungiyar AES”. Haka kuma wannan zaman taro na da manufar tattara dukkan masu ruwa da tsaki na bangaren makamashi a cikin shiyyar yankin Sahel domin yin musanyar ra'ayoyi da kuma yin musanyar kwarewa da tattauna kalubalen hadin gwiwa dake da nasaba da samar da makamashi.

Kamfanonin wutar lamtarki na mambobin kungiyar kasashen yankin Sahel za su raba kwarewarsu da kuma gabatar da shawarwarin kawo sauyi cikin zamani ta yadda za'a amsa bukatun al'umomin shiyyar kasashen yankin Sahel.

A tsawon wadannan kwanaki uku, akwai mahawarori daban daban da tarukan karawa juna sani kan mau’du'in wannan shekara.

Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.