logo

HAUSA

Ma’aikatar ’yan sanda ta PJ ta kama wani gungun barayi a birnin Yamai

2024-02-18 13:31:52 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, a ranar jiya Asabar 17 ga watan Fabrairun shekarar 2024, ’yan sanda a birnin Yamai sun kama barayin dake farma mutanen da suka je daukar kudi a banki, bayan da mutanen dake mu’amala da bankuna suka kai kukansu a ofishin ’yan sanda na PJ.

Daga birnin na Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Wani gungun ne dake kunshe da mutum biyu, guda dan asalin Nijar, kana gudan kuma dan asilin tarayyar Nijeriya. Na farko yana da shekara 38 da haifuwa, yayin da na biyun lattijo ne mai shekara 58 da haifuwa.

Bisa ga yawan korafe-korafen mutane ne, ’yan sandan birnin Yamai suka gudanar da bincike bayan sun karbi kararraki fiye da goma sha uku.

’Yan sandan sun gabatar da barayin biyu gaban ’yan jarida a ranar jiya Asabar, a jimilce miyagun mutanen biyu sun tafka sata 13 tare da taxi biyu da suke amfani da su, kuma dukkan wadannan sace-sace sun faru ne a birnin Yamai, kuma miliyan hamsin da biyar na Sefa (55) wadannan barayi biyu suka kwace daga hannun mazauna birnin Yamai, a cewar ma’aikatar ’yan sanda ta PJ.

Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.