logo

HAUSA

Firaministan Isra’ila: Ta hanyar tattaunawa kai tsaye ne kadai za a iya warware rikicin Falasdinu da Isra’ila

2024-02-18 15:27:10 CMG Hausa

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana jiya Asabar cewa, ba za a iya warware rikicin Falasdinu da Isra’ila ba, sai an komawa tattaunawa kai tsaye, ba kuma tare da gindaya sharudda ba, kana ya nanata adawarsa da amincewa da kafuwar kasar Falasdinu.

Game da taron tattaunawar da aka gudanar a birnin Alkahirar Masar, kan batutuwan musayar mutanen da ake tsare da su, da tsagaita bude wuta a Gaza, Netanyahu ya bayyana cewa, matsayin Hamas bai sauya ba, shi ya sa tawagar Isra’ila ta fice daga taron na Masar. Ya ce sai Hamas ta sauya matsayi, Isra’ila za ta sake komawa teburin tattaunawa.

A sa’i daya kuma, Netanyahu ya jadadda cewa, Isra’ila za ta ci gaba da yin yaki a Gaza, har sai ta cimma nasara baki daya. Ya ce, mutanen dake son hana ayyukan da Isra’ila ke gudanarwa a birnin Rafah dake kudancin Gaza, suna fatan Isra’ila ta rasa yakin ne, kuma ba zai yarda da a yi haka ba. (Safiyah Ma)