logo

HAUSA

Shugaban hukumar zartaswar AU ya bayyana damuwa game da yawaitar kalubalen tsaro a Afirka

2024-02-18 16:17:21 CMG Hausa

 

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana damuwa game da yawaitar kalubalen tsaro a sassan Afirka.

Moussa Faki Mahamat, wanda ya yi tsokacin a jiya Asabar, yayin taron kolin AU karo na 37 da aka bude a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, ya bayyana matukar damuwa game da yawan sauye-sauyen gwamnatoci da ake samu, da rashin daidaiton siyasa da jagoranci, baya ga kalubalen sauyin yanayi, da koma-bayan tattalin arziki a sassan nahiyar.

Ya ce, nahiyar Afirka na shan fama da matsalar kashe makudan kudade a fannin ayyukan soji, a gabar da ‘yan ta’adda, da tashe-tashen hankula ke wargaza wasu sassa na nahiyar, suna haifar da koma-baya ga muhimman ginshikan ci gabanta.

A wani ci gaban kuma, shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Cheikh Ghazouani, ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ta AU na karba-karba yayin bude taron kolin karo na 37.

Ghazouani ya maye gurbin shugaban Comoros Azali Assoumani, wanda ya rike ragamar kungiyar tun daga watan Fabrairun bara, yayin bude taron kolin kungiyar karo na 36.

Cikin jawabinsa na kama aiki, shugaban na Mauritania ya bayyana bukatar cimma muradun da suka haifar da kafuwar kungiyar ta AU, musamman bukatar ‘yantar da Afirka ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki, da hadin kai da samar da wadata.    (Saminu Alhassan)