Wang Yi: Sin ta sha alwashin zama jigon samar da daidaito a duniya mai tangal-tangal
2024-02-18 15:54:12 CMG Hausa
Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kana ministan wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi mai taken “Sin ta sha alwashin zama jigon samar da daidaito a duniya mai tangal-tangal”. Wang ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar taron tsaron Munich a jiya Asabar.
Wang Yi ya bayyana cewa, duniya na fama da hargitsi, kuma bil adam na fuskantar kalubaloli daban daban. Kazalika ra’ayin ba da kariya da kallon dukkanin matsaloli ta mahangar tsaro, sun haifar da illa ga tattalin arzikin duniya, yayin da kuma ra’ayin bangare guda, da siyasar gungun bangarori ke gurgunta tsarin cudanyar kasa da kasa.
Har ila yau, rikicin Ukraine ya ci gaba da tabarbarewa, kuma rikicin Gabas ta tsakiya ya sake barkewa. Fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, da sauyin yanayi, da tirka-tirka game da harkokin da suka shafi binciken sararin samaniya, da sauran kalubaloli na aukuwa daya bayan daya. Amma duk da sauyin yanayin kasa da kasa, a matsayin babbar kasa mai dauke da babban nauyi, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da manufofinta cikin kwanciyar hankali. Sin ta sha alwashin zama jigon samar da daidaito a duniya mai tangal-tangal.
Daga nan sai ya bayyana bukatu da ake da su a fannoni guda hudu. Da farko dai, za ta zama jigon samar da daidaito a lokacin da ake inganta hadin gwiwa tsakanin manyan kasashen duniya. Sannan za ta zama jigon samar da daidaito a lokacin da ake tinkarar batutuwa da dumi-dumi. Bugu da kari, za ta zama jigon samar da daidaito a lokacin da ake gudanar da harkokin kasa da kasa. Daga karshe dai, za ta zama jigon samar da daidaito wajen karfafa ci gaban duk duniya baki daya. (Safiyah Ma)