logo

HAUSA

Bikin Bazara Na Shekarar Loong: Alkaluma Sun Bayyana Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin

2024-02-18 21:40:40 CMG Hausa

Jaridar El Mundo ta kasar Sifaniya, ta wallafa a shafinta game da bikin Bazara na gargajiyar kasar Sin, cewa wa’adin hutun murnar bikin Bazara, lokacin hutu ne mafi muhimmanci a kasar Sin. Irin wannan lokaci, na baiwa Sinawa damar kashe makudan kudade, kuma bikin na zama ma’auni na gwada ci gaban tattalin arziki.

To ko ta yaya tattalin arzikin kasar Sin yake a lokacin hutun murnar bikin Bazara na shekarar Loong a bana?

Yawan zirga-zirgar mutanen da suka yi tafiye-tafiye a sassan kasar Sin ya kai miliyan 474, kuma yawan kudaden da suka kashe ya zarce dalar Amurka biliyan 87 da miliyan 951, adadin da suka karu da 34.3% da kuma 47.3% bisa na bara. Har ila yau, yawan zirga-zirgar mutanen da suka fita da kuma shigo kasar Sin ya kai miliyan 13 da dubu 517, adadin ya kai miliyan 1 da dubu 690 a ko wace rana, wanda ya karu da sau 2.8 bisa na makamancin lokaci na bara.

A tsawon lokacin hutun na kwanaki 8, yawan kudaden da aka kashe wajen sayen tikitocin kallon sinima ya wuce dallar Amurka biliyan 1 da miliyan 112, wanda ya kafa tarihi a lokacin hutun murnar bikin Bazara. Kana kasuwar sayayya ta samu tagomashi a kasar Sin a lokacin hutun murnar bikin na Bazara, lamarin da ya kaddamar da ci gaban tattalin arzikin kasar a shekarar Loong.

Da ganin yadda aka yi sayayyya a lokacin hutun, ana iya gano babbar kasuwar kasar Sin, da kuma kara fahimtar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. A karshen watan Janairun bana, asusun IMF ya daga hasashen saurin karuwar tattalin arzikin Sin na shekarar 2024 zuwa 4.6%. Kasar Sin tana da karfin gwiwar ci gaba da farfado da tattalin arzikinta da ci gaba da zuba kuzari ga duniya, sakamakon yadda kasuwarta ta samu tagomashi, da kuma rika samun ginshikan ci gaban tattalin arziki masu inganci. (Tasallah Yuan)