logo

HAUSA

An bude taron Munich kan harkokin tsaro

2024-02-17 17:08:29 CMG Hausa

A jiya Juma’a ne aka bude taron Munich na tattauna batutuwan tsaro karo na 60 ko MSC a takaice, taron da ya mayar da hankali ga kiraye-kirayen bunkasa hadin gwiwa, da inganta jagorancin duniya.

Cikin jawabinsa na bude taron, shugaban dandalin Christoph Heusgen, ya bayyana fatan ganin mahalarta sun lalubo bakin zare, game da muhimman kalubalen tsaro dake addabar duniya, musamman duba da yadda ake samun karin yanayi na zaman-doya-da-man ja tsakanin sassan yankunan duniya, da karin rashin tabbas a fannin tattalin arziki.

Ana dai fatan tattauna batutuwan da suka shafi rikicin Ukraine, da na  Isra’ila da Hamas yayin taron na yini 3.

Tun a shekarar 1963 ne dai aka kafa dandalin na MSC, a matsayin dandalin kasa da kasa, na tattauna manyan batutuwan tsaro dake addabar duniya, kana ya zamo wuri da ake fitar da manufofin diflomasiyya don warware matsalolin tsaro. (Saminu Alhassan)