logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na kasar Amurka

2024-02-17 16:55:54 CMG Hausa

Jiya Jumma’a 16 ga wata ne, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a yayin da suke halartar taro kan harkokin tsaro a birnin Munich na kasar Jamus.

Jami’in na kasar Sin ya ce, shugaba Xi Jinping da shugaba Biden sun gana a karshen shekarar bara, inda suka yi musanyar ra’ayi kan wasu muhimman fannoni na dangantakar kasashen biyu, tare da cimma maslaha. Ya ce babban aikin dake gabansu a halin yanzu shi ne, tabbatar da “Mahangar San Francisco” a zahiri, da raya dangantakar Sin da Amurka cikin dogon lokaci kuma ta hanyar da ta dace.

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kana, Taiwan, wani bangare ne da ba za’a iya ware shi daga babban yankin kasar Sin ba. Wannan shi ne hakikanin halin da ake ciki game da batun Taiwan.

Kaza lika, Wang ya ce yunkurin korar kasar Sin bisa hujjar kawar da hadari, gami da yunkurin mayar da kasar Sin saniyar ware, ko kuma katse mu’amala da ita da kasar Amurka ke yi, zai lahanta ita kanta Amurka. Wang ya kuma bukaci Amurka da ta soke takunkumin da ta sanyawa wasu kamfanoni, gami daidaikun mutane na kasar Sin ba bisa doka ba, don kaucewa illata hakkokin kasar Sin na samun ci gaba.

Bangarorin biyu sun kuma tattauna kan yadda za su kara mu’amala a matakai daban-daban a nan gana, da cimma matsayar ci gaba da yin mu’amala tsakanin su, da ci gaba da aiwatar da “Mahangar San Francisco”. (Murtala Zhang)