logo

HAUSA

An bude taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU karo na 37

2024-02-17 21:23:09 CMG Hausa

A yau Asabar 17 ga wata ne aka bude taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU karo na 37 a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha. Taron na yini biyu, wanda ya hallara jagororin kasashen Afirka mambobin kungiyar ta AU, a bana yana da taken "Ilmantar da dan Afirka daidai da bukatar karni na 21: Gina tsarin samar da ilimi mai juriya, da fadada damar shigar da kowa, da samar da ilimi mai nagarta na tsawon rayuwa ga daukacin al’ummar Afirka".

Baya ga taken taron na shekarar bana, ana fatan shugabannin nahiyar mahalartansa, za su tattauna game da batutuwan da suka shafi nahiyar, ciki har da batun wanzar da tsaro da zaman lafiyar shiyyoyi zuwa batun bunkasar nahiyar, da batun sauye sauye ga kungiyar ta AU, da burin nahiyar Afirka na kara taka rawar gani a harkokin kasa da kasa.(Saminu Alhassan)