logo

HAUSA

Liu Jianchao ya halarci babban taron kafa dandalin tattaunawa na jam’iyyun siyasar kasa da kasa mai taken “yaki da sabon ra’ayin mulkin mallaka”

2024-02-17 16:59:36 CMG Hausa

Shugaban sashin tuntubar kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Liu Jianchao, ya jagoranci tawagar jam’iyyar kwaminis zuwa kasar Rasha a jiya Jumma’a 16 ga watan nan, don halartar babban taron kafa dandalin tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasar kasa da kasa, mai taken “yaki da sabon ra’ayin mulkin mallaka”, tare da gabatar da jawabi.

Jami’in ya ce, har yanzu ana samun bullar nau’o’in mulkin mallaka a duk fadin duniya, abun dake haifar da illa sosai ga duniya. Don haka ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kare hakkokinsu na samar da ci gaba, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da taimakawa ga cudanyar mabambantan wayewar kai, da kawo sauyi ga tsarin tafiyar da harkokin duniya, tare da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

A yayin taron, jami’in ya kuma gana da shugaban jam’iyyar United Russia, Dmitry Medvedev. (Murtala Zhang)