logo

HAUSA

Wang Yi: Kamata ya yi Sin da Birtaniya su bunkasa musaya da hadin gwiwa tare da shawo kan sabanin siyasa

2024-02-17 17:11:31 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga bangarorin Sin da Birtaniya, da su karfafa musaya da hadin gwiwa, kana su warware sabani da rigingimu ta hanyar da ta dace. Har ila yau su yi kokarin maido da alakar dake tsakanin su kan turba ta gari, tare da aiwatar da manufofin samar da ci gaba bisa daidaito.

Wang, ya yi kiran ne a jiya Juma’a, yayin da yake ganawa da sakataren harkokin wajen Birtaniya David Cameron, a gefen taron tsaro na Munich dake gudana. Ya ce yayin da ake tsaka da fuskantar kalubalolin tsaro a duniya, kamar farfadowar tunanin yakin cacar baka, da kariyar ciniki, da tafiyar hawainiyar farfadowar tattalin arziki, a matsayinsu na mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD, kamata ya yi Sin da Birtaniya su karfafa tattaunawa, su kuma taka rawar gani wajen yayata matakan wanzar da zaman lafiya da lumana.

A nasa bangare kuwa, mista Cameron cewa ya yi Birtaniya na fatan kallon alakar ta da Sin daga babbar mahanga, tana kuma da burin bunkasa dangantakar yadda ya kamata, kana za ta ba da hadin kai wajen ganin sassan biyu sun kawar da bambance bambancen dake tsakaninsu da warware matsaloli bisa martaba juna.  (Saminu Alhassan)