logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da matakan kawo karshen matsalolin rikicin Fulani da Manoma a kasar

2024-02-17 16:25:51 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara aiwatar da sabon shirin PULAKU wanda zai mayar da hankali wajen samar da matsugunai da hanyoyin mota da makarantu da sauran mahimman ababen more rayuwa ga Fulani da manoma.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da kwamitin aiwatar da shirin a birnin Abuja, ministan gidaje da raya birane na kasar ne zai jagoranci kwamitin wanda yake da wakilcin wasu daga cikin gwamnonin jahohin arewacin kasar .

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shi dai wannan shiri zai shafi yankunan da aka fi samun yawan fitintinu tsakanin Fulani da manoma musamman a shiyyar arewacin kasar.

Jihohin da za su amfana sun hada da Sokoto da Kebbi da Katsina da Zamfara da Niger da Kaduna da kuma jihar Benue.

Mataimakin shugaban kasan ya ce yana da tabbacin shirin zai taimaka wajen warware matsalolin hare haren `yan ta`adda da talauci musamman a tsakanin al`umomin da ke rayuwa a shiyyar arewacin Najeriya.

A tattaunawarsa da manema labarai jim kadan da kaddamar da kwamitin, gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani cewa yake.“ Shirin Pulaku da aka samar cigaba ne sosai, muna murna da shi, domin kuwa tabbas zai taimaka wajen warware matsalolin mutanen da wani yanayi ya sanya suka kauracewa muhallansu, wanda da yawansu yanzu ba su da wajen zama sabo da tashe-tashen hankula”

Shi kuwa gwamnan jihar Katsina Dr Umar Dikko Radda cewa ya yi,“Wannan daya ne daga cikin matakan lalama da ake bi wajen tabbatar da zaman lafiya, kuma ina ganin cewa yana da muhimmanci idan aka yi amfani da karfi wani lokaci kuma sai a shigo da dabarun masalaha domin dai mu warware mastalolin da suke addabar al`ummar mu.”(Garba Abdullahi Bagwai)