logo

HAUSA

Tsohon shugaba Issoufou Mahamadou na halartar wata haduwa kan Zlecaf a birnin Addis Ababa na kasar Habasha

2024-02-16 16:24:52 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar, bisa goron gayyatar shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka AU, tsohon shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou, zakaran yankin ciniki mara shinge na Afrika ZLECAF, ya isa ranar jiya 15 ga wata a kasar Habasha domin taron ZLECAF daga ranar 17 zuwa 18 ga watan Fabrairun shekarar 2024 a birnin Addis Ababa.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Wannan tafiya ta tsohon shugaba Issoufou Mahamadou a kasar Habasha ta biyo bayan goron gayyatar ranar 8 ga watan Fabrairu da Moussa Faki Mahamat da kansa ya yi masa domin halartar wani taron shimfida na ZLECAF da zai gudana a daura da dandalin tarayyar Afrika na AU.

Tsohon shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou da kansa ne zai halarci wannan muhimmiyyar haduwa da ke cikin tsarin ajandar zaman taro karo na 37 na kungiyar AU tare da sauran shugabannin kasashen Afirka.

Sai dai wannan karramawa da aka yi wa tsohon shugaban Nijar na fita daga kasar domin halartar wannan haduwa ta janyo cece kuce da zazzafar mahawara a tsakanin 'yan kasar Nijar ganin cewa tsohon shugaban kasar na daga cikin tsoffin shugabannin kasa da suka tura Nijar cikin halin da ta shiga, tun bayan lamarin da ya janyo juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023.

A cewar shugaban kwamitin AU, tsohon shugaban kasar Nijar yayi aiki tukuru wajen kafa kasuwa guda ta Afirka ZLECAF, bisa jajircewarsa a fagen duniya na ganin shige da fice cikin ‘yanci da walwala sun tabbata, bisa haka ne, Issoufou Mahamadou yake halartar wannan taro a matsayinsa na zakaran ZLECAF.