logo

HAUSA

Minister : Najeriya za ta dakatar da tallafin wutar lantarki

2024-02-16 17:21:40 CMG Hausa

Najeriya ta bayyana shirin kawo karshen tallafin wutar lantarki a wani gagarumin sauyin manufa da nufin magance kalubalen tattalin arziki.

Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu ya shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, a ranar Laraba cewa, matakin ya biyo bayan rashin samun wutar lantarki da ake fama da shi a kasar ne, sakamakon batutuwa da dama da suka hada da basussukan tallafi da ake bayarwa, da matsin lamba na yin garambawul a bangaren makamashin kasar da kuma inganta dorewar kasafin kudi.

Ya ce a yanzu za a bar gwamnatocin jihohi su rika samar da wutar lantarki ga jihohinsu da kansu, yana mai jaddada cewa shirin cire tallafin na daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na daidaita ayyuka da samar da inganci a fannin wutar lantarki.

Sanarwar dai ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke nuna damuwarsu kan illar cire tallafin ga kasafin kudin jama’a, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen tattalin arziki. Wasu kuma na kallon hakan a matsayin matakin da ya dace don samun ci gaba mai dorewa da kuma inganta amincin samar da wutar lantarki a fadin kasar. (Yahaya)