logo

HAUSA

Hadin gwiwar taron gwamnoni tare da shugaban tarayyar Najeriya ya nuna kin amincewa da shigo da kayan abinci daga waje

2024-02-16 15:52:48 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da taron gaggawa da daukacin gwamnonin kasar a kan halin da kasar ke ciki na tsadar kayan abinci da sauran matsalolin rayuwa da al`ummar kasar ke fuskanta.

Yayin taron shugaban na tarayyar Najeriya ya bukaci gwamnonin da su mayar da hankali sosai wajen saka jari a fannonin da suka shafi noma tare kuma da bullo da saukakan matakan tallafawa manoma.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Bayan kammala taron na jiya, ministan labarai da wayar da kan jama’a na kasar Alhaji Muhammed Idris ya yi wa manema labarai karin bayani a game da kudurorin da taron ya zartar.

“Na farko an umarci mashawarcin shugaban kasa a kan sha`anin tsaro da darakta janar na hukumar tsaro ta DSS da Sefeto janar na `yan sandan kasar da su hadu da gwamnonin jihohi domin duba batun masu boye kayan abinci a daidai lokacin da kasar ke matukar bukatar a fito da abinci ga `yan kasa ta yadda za a daidaita farashin kayayaki”.

“Na biyu kuma a yanke shawarar cewa domin cigaban kasar nan, ba ma bukatar a rinka shigo da abinci daga waje a wannan yanayi, Najeriya tana da karfin da za ta iya ciyar da kanta har ma ta fitar zuwa wasu kasashe”

A bangaren tsaro kuma taron ya bayyana gamsuwa bisa irin ci gaba da yanzu haka aka samu, amma duk da haka dai,“Gwamnatin tarayyar da kuma gwamnatocin jihohin suna duba yiwuwar samar da `yan sandan jihohi, ko da yake wannan batu ne da ke bukatar a fadada tattaunawa a kan sa, amma dai gwamnatocin biyu sun amince da yiwuwar samar da `yan sandan jihohin” (Garba Abdullahi Bagwai)