logo

HAUSA

Majalisar tsarin mulkin Senegal ta soke dokar dage zaben shugaban kasa

2024-02-16 17:09:17 CMG Hausa

Majalisar tsarin mulkin Senegal ta sanar a jiya Alhamis cewa ta soke dokar dage zaben shugaban kasar da shugaba Macky Sall ya kafa a ranar 3 ga watan Fabrairu.

A cikin wata takardar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu, majalisar tsarin mulkin kasar ta bayyana cewa, dokar da majalisar dokokin kasar ta amince da ita a ranar 5 ga watan Fabrairu, wadda ta dage zaben daga ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa 15 ga Disamba, ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar. Ganin cewa, “wai ba shi yiwuwa a shirya zaben shugaban kasa a ranar da aka kayyade da farko,” majalisar tsarin mulkin kasar ta yi kira ga hukumomi da su gudanar da zaben nan ba da jimawa ba.

A ranar 3 ga watan Fabrairu ne shugaban kasar ya sanar da dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairu, a wani sako da ya aikewa al'ummar kasar sa'o'i kadan kafin fara yakin neman zabensa. A ranar 5 ga watan Fabrairu ne majalisar dokokin kasar Senegal ta amince da kudurin dage zaben shugaban kasar zuwa ranar 15 ga watan Disamba na wannan shekara. (Yahaya)