logo

HAUSA

Jakadan Sin Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Game Da Ba Da Gudummawar Shawo Kan Rikicin Siyasar Yemen

2024-02-15 16:39:56 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya jaddada aniyar kasar Sin, ta yin hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, wajen shawo kan rikicin siyasar dake addabar kasar Yemen, da nufin wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin Gabas ta Tsakiya.

Yayin taron kwamitin tsaron MDD da ya gudana a jiya Laraba, don gane da batun kasar ta Yemen, Zhang Jun ya yi karin haske game da tattaunawar dake gudana tsakanin sassan masu ruwa da tsaki, don gane da shawo kan rikicin Yemen ta hanyar siyasa, inda ya ce, ana samun ci gaba, ko da yake akwai bukatar hada karfi da karfe wajen rage radadin yanayin da al’ummar Yemen din ke ciki.

A daya bangaren kuma, Zhang Jun ya nuna damuwa game da yanayin zaman dar dar da ake fuskanta a baya-bayan nan a yankin tekun Maliya, musamman matakan soji da wasu kasashe ke aiwatarwa kan Yemen. Ya ce, ya kamata dakarun Houthi su gaggauta dakatar da kaddamar da hare-hare kan jiragen ruwan dakon kayayyakin kasuwanci, ya kuma jaddada cewa, har yanzu kwamitin tsaron MDD bai ba da iznin amfani da karfin tuwo kan Yemen ba.

Daga nan sai ya kara tabbatar da goyon bayan kasar Sin ga jagoranci mai ‘yanci na Yemen, wanda zai samar da damar warware matsalar kasar a siyasance, da karfafa gwiwar sassan kasa da kasa, wajen bayar da tallafin wanzar da zaman lafiya mai dorewa. (Saminu Alhassan)