logo

HAUSA

An mai da hankali ga matakan wanzar da zaman lafiya a Afirka yayin taron majalisar gudanarwar AU

2024-02-15 16:06:15 CMG Hausa

An bude taron majalisar gudanarwar kungiyar AU karo na 44, wanda zai gudana a tsawon yini biyu, a birnin Addis Ababan kasar Habasha, inda aka mai da hankali ga batutuwan dake shafar zaman lafiya a yankin, da ba da ilmi, da tsarin cudanyar bangarori daban daban na duniya da sauransu.

Yayin bikin bude taron a jiya Laraba, shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya waiwayi nasarori, da matsaloli da aka samu a cikin shekaru 10 na farkon ajandar shekarar 2063 ta kungiyar AU, wato daga shekarar 2014 zuwa 2023. Moussa Faki ya bayyana cewa, juyin mulkin soja, da rikice-rikice kafin ko bayan zaben shugabannin kasashen yankin, da matsalar jin kai a sakamakon yake-yake, da tasirin sauyin yanayi, dukkansu na barazana ga bunkasuwar nahiyar Afirka.

Ya ce, yayin da ake shiga shekaru 10 karo na biyu na ajandar, ya kamata kasashe mambobin kungiyar su yi kokari tare, don cimma burin samun bunkasuwa na kungiyar AU.

A nasa jawabi kuwa, sakataren gudanarwar hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD Claver Gatete, cewa ya yi ba da ilmi yana da muhimmanci ga bunkasuwar Afirka, don haka ya yi kira da a yi kwaskwarima ga tsarin ba da ilmi a Afirka, da kara horas da kwararru, da kyautata tsarin ba da ilmi ta hanyar fasahar zamani don biyan bukatun bunkasuwar Afirka. (Zainab)