Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta samar da jami’an tsaro da za su rinka kare manoma a gonakin su
2024-02-15 15:45:40 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kafa hukumar da za ta rinka daidaita farashin kayayyaki, a wani mataki na rage karuwar hauhauwar farashin kayan abinci a kasar.
Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja yayin wani babban taron masu ruwa da tsaki na tsawon yini biyu da aka shirya a kan sauyin yanayi, tsarin samar da abinci da kuma alkinta albarkatu.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mataimakin shugaban kasan ya ce idan an samar da hukumar, ita za ta kasance da alhakin fito da tsare tsaren daidaita farashin kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi, har ila yau za ta rinka kula da runbunan ajiyar kayan abinci mallakin gwamnati.
Ya ci gaba da cewa, wannan mataki da za a dauka daya ne daga cikin sabbin sauye-sauyen manufofin gwamnati na tabbatar da wadatar abinci da kuma ruwan sha ga ‘yan Najeriya cikin sauki.
“Gwamnatin tarayyar ta himmatu sosai wajen taimakawa kananan manoma ta hanyar shirye-shiryen bayar da tallafi daban daban domin dai karfafa musu gwiwar noman abinci, yin haka zai kasance wata hanya da za ta tabbatar da farfado da filayen noma.”
Mataimakin Shugaban kasar ya ce a yanzu haka akwai sabbin filaye masu fadin hekta dubu dari 5 wanda za a yi amfani da su wajen noman abinci, haka kamar yadda ya ce zai yi matukar tasirin gaske ga wadatuwar abinci a kasa baki daya.
Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da da cewa, gwamnati tana hada kai da kamfanonin gine-gine domin su gudanar da akin sare dazuzzuka, ta yadda za a samu damar yin noma a cikin su.
A kan kalubalen tsaro kuwa wanda ya yi sanadin hana dubban manoma komawa gonakinsu, mataimakin shugaban kasar ya shaidawa mahalarta taron cewa,
“Ina son na ba ku tabbacin cewa, za mu yi amfani da matakan tsaronmu wajen kare gonaki da manoman kansu, ta yadda manoman za su samu damar komawa gonakinsu ba tare da fargabar za a kai masu hari ba.”(Garba Abdullahi Bagwai)