logo

HAUSA

Yadda Abubuwan Mamaki Ke Faruwa a gasar AFCON 2023

2024-02-15 16:29:48 CGTN HAUSA

Kawo yanzu an kammala wasannin kasashe 16 kuma a yau za a fara wasannin kusa da na kusa da na karshe a wasannin da kasar Ibory Coast take karbar bakunci ta gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 34 a tarihi.

Tuni aka samu kasashe guda takwas da za su fafata a zagayen kusa da na kusa da na karshe a gasar kuma gasar tana ci gaba da baI wa marada kunya tare da ba da mamaki ganin yadda manyan kasashe suke shan kashi a hannun kasashen da ba a yi tsammani ba.

 Kawo yanzu kasashen da suka kai matakin kusa da na kusa da na karshe sun hada da tawagar Super Eagles ta Nijeriya sai mai masaukin baki Ibory Coast wadda ta doke mai kare kambu wato Senegal, sai kuma kasar Angola wadda itama tana nuna bajinta a wannan gasar.

 Kasashen Congo da Guinea ma sun samu damar tsallakawa zuwa mataki na gaba sai kuma kasashen Cape Berde da Afirka ta Kudu da Mali duka sun samu damar tsallakawa zuwa mataki na gaba wanda mataki ne da yake da matukar hatsari.

 NIJERIYA DA ANGOLA

 Tawagar kwallon kafa ta Nijeriya ta kai zagayen dab da na kusa da na karshe, bayan doke Kamaru da ci 2-0 a wasan zagaye na biyu a gasar kofin Afirka kuma tun kafin hutu, Super Eagles ta ci kwallon farko ta hannun Ademola Lookman, sannan kafin nan an soke wadda Semi Ajayi ya fara cin Kamaru wadda aka ce ya yi satar gida.

 Bayan da aka yi hutu ne aka koma zagaye na biyu Kamaru ta yi ta kokarin farke kwallon da aka zura mata, amma ba ta samu dama da yawa ba, sannan dab da za a tashi daga wasan ne Super Eagles ta kara ta biyu ta hannun Ademola Lookman, hakan ya sa tawagarta kai zagayen kusada da na kusa da na karshe.

 Da wannan sakamakon Nijeriya za ta fafata a zagayen dab da na kusa da na karshe da Angola yau Juma’a 2 ga watan Fabrairu, kuma gabanin fafatawar Nijeriya da Kamarun a ranar Asabar, Angola ta doke Namibia 3-0 a wasan farko a zagaye na biyu na wasannin da ake buga wa a Ibory Coast.

 Nijeriya mai kofin Afirka uku jimilla ta yi nasara a kan Kamaru karo na uku a babbar gasar tamaula ta Afirka da suka hadu a baya-bayan nan saboda Super Eagles ta yi nasara a kan Kamaru a zagayen kuarter finals a 2004 da aka yi a Tunisia, sannan Nijeriya ta doke Kamaru 3-2 a wasannin da aka gudanar a Masar a 2019.

 Nijeriya ta kawo matakin zagaye na biyu a Ibory Coast, bayan da ta yi ta biyu a rukunin farko da maki bakwai, iri daya da na Ekuatorial Guinea, wadda ta yi ta daya bayan ta yi raga-raga da mai masaukin baki.

 Super Eagles ta hada maki bakwai ne, bayan tashi 1-1 da Ekuatorial Guinea a wasan farko a rukuni na daya da cin Ibory Coast 1-0 da kuma nasara a kan Guinea – Bissau 1-0.

 Ita kuwa Kamaru ta yi ta biyu ne a rukuni na uku, bayan da ta yi 1-1 da Guinea da rashin nasara 3-1 a hannun Senegal, sannan ta doke Gambia 3-2 kuma Kamaru mai AFCON biyar ta fara da lashe kofin Afirka a kan Nijeriya a 1984 da cin 3-1 da kuma 1988 da ta yi nasarar cin 1-0 da kuma a 2000 da suka tashi 2-2, Kamaru ta lashe kofin a bugun fenariti 4-3 a Nijeriya.

 CONGO DA GUINEA

 Tabbas abin mamaki ne a ce tawagar ‘yan wasan Congo ta iya yin karfin hali ta doke ta Masar a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan sun tashi wasa 1-1 kuma wasa ne wanda za a iya cewa an yi kare jini biri jini wanda sai da ta kai an yi minti 120 ana gwabzawa.

 Kasar Masar ita ce wadda tafi kowacce kasa yawan lashe kofin a tarihi domin ita ce ta lashe sau bakwai wanda hakan ya sa ake ganin tana da tarihi mai kyau a gasar wanda kuma yake taimaka mata a duk lokacin da aka zo buga gasar.

 Doke kasar Masar da Congo ta yi ya nuna cewa tabbas karfi ya kawo kuma kasar ta Congo, wadda ta yi ta biyu da maki uku a cikin rukunin da ya hada da Morocco da Zambia da kuma Tanzania za ta iya kai wa matakin da ba a yi zato ba a yanzu.

 Sai dai itama Guinea ba kanwar lasa bace domin ta uku ta yi a cikin rukunin da ya hada da mai kare kambu Senegal da Kamaru da kuma Gambia kuma ta hada maki hudu ne wanda hakan ya bata damar fitowa daga cikin rukunin.

 Sannan bayan fitowarta ta hadu da takwararta ta Ekuatorial Guinea kuma ta doke ta wanda hakan ya sa ake ganin ita ma za ta iya ba da mamaki a wasan da za ta kece raini da Congo, wasa ne wanda za a fafata a filin wasa na Stade Olympikue Alassane Ouattara.

   MALI DA IBORY COAST

 Mali, wadda ta fito daga cikin rukunin da ya hada da Afirka ta Kudu da Namibia da Tunisia ita ce ta yi ta daya a cikin nrukunin kuma tana da matasan ‘yan wasa, sannan kuma kokarin da ta yi ta doke kasar Burkina Faso

 Masu masaukin baki Ibory Coast sun shammaci duniya, sun fito a matsayin ‘yan alfarma kuma sun doke kasar Senegal, mai kare kambu, wadda take da manyan ‘yan wasa irinsu Sadio Mane da Khalilou Koulibally da Michael Jackson da sauransu.

 Har ila yau, Ibory Coast wadda take karbar bakunci tana da zakakuran ‘yan wasa irinsu Ibrahim Sangare da Frankie Kessie da Fofana da sauransu za ta iya lashe kofin kasancewar ta a gida kuma tana da karfin lashe wasa duk da cewa ta kori kociyanta sakamakon rashin tabuka abin a zo a gani.

CAPE BERDE DA AFIRKA Ta Kudu

 Kasar Cape Berde, wadda ta ba wa duniya mamaki a wannan gasar ta fito a cikin rukunin da ya hada da manyan kasashe irinsu Ghana, mai kofin Afirka guda biyar, da Masar, wadda ta fi kowacce kasa lashe kofin da guda bakwai sai kuma Mozambikue, kuma haka ta ba wa duniya mamaki.

 A wasa na farko Cape Berde ta doke kasar Ghana da ci 2-1 sannan ta doke kasar Mozambikue da ci uku babu ko daya sai kuma suka buga 2-2 da kasar Masar, hakan ya sa ake ganin tabbas Cape Berde za ta ba wa mutane mamaki ko kuma ma ta iya lashe kofin duk da cewa akwai manyan kasashe irinsu Nijeriya da Ibory Coast da sauransu.

 Sai dai itama Afirka ta Kudu ba karamin bajinta ta nun aba musamman wajen fitowa daga cikin rukunin da ya hada da Mali da Namibia da Tunisia kuma ta doke tawagar ‘yan wasan kasar Morocco wadda ake ganin babu tawaga mai karfinta a Afirka idan aka kalli bajintar da suka nuna a gasar cin kofin duniya.