logo

HAUSA

Matan gwamnoni a tarayyar Najeriya sun sha alwashin taimakawa hukumar yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kasar

2024-02-14 15:54:33 CMG Hausa

Kungiyar matan gwamnoni a tarayyar Najeriya ta tabbatar da aniyarta wajen bayar da gudummawa ga fafutukar da hukumar yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kasar ke yi wajen kawo karshen matsalolin ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin al’ummar kasar.

Shugabar kungiyar kuma uwargidan gwamnan jihar Kwara Ambasardor Olufolake Abdulrazaq ce ta tabbatar da hakan a karshen taron karawa juna sani kan dabarun kare al’umma daga nuna sha’awar sha ko kuma safarar miyagun kwayoyi wanda hukumar ta NDLEA ta shiryawa matan gwamnonin a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugabar kungiyar matan gwamnonin ta kuma nuna bukatar gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta baci a kan amfani da muggan kwayoyi da kuma safarar su, ta hanyar daukar dukkan matakan da suka kamata tun daga na samar da kayan aiki irin zamani ga jami’an hukumar da kuma amfani da shawarwarin kwararru.

Uwargidan gwamnan na jihar Kwara ta shaidawa hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyin ta Najeriya cewa, daukacin matan gwamnonin za su goyi bayan shirin gina a kalla cibiyoyin da za a rinka killace matasan da suka kamu da annobar shan miyagun kwayoyi a kowanne shiyya na dan majalisar dattawa domin rage wahalhalun tsadar magani da kuma nuna kyama da ake yiwa irin wadannan matasa a cikin al’umma.

“Wannan taro da aka gudanar da zai kara sa mu fahimci tsarin yaki da miyagun kwayoyi na kasa da kuma haska mana rawar da za mu taka a kwamatin lura da muggan kwayoyi a jahohi, kana kuma ya kara ilimantar da mu a kan yadda za mu kara azama wajen riga-kafin yawan ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma kula da masu ta’ammali da kwayoyin.”

A nasa jawabin, shugaban hukumar ta NDLEA Birgediya janar Buba Marwa mai ritaya godiya ya yi ga matan gwamnonin bisa damar da suka samu suka halarci taron duk da hidindimun dake gabansu.

“Ina kara jaddada kirana a gare ku da ku taimaka ku shigo tare da wayar da kan duk wani mai ruwa da tsaki a jahohinku domin su bayar da gudummawarsu a fafutukar da ake yi na kawo karshen wannan matsala.”(Garba Abdullahi Bagwai)