logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasashe masu ci gaba da su kara samar da gudummawar jin kai ga kasashe masu tasowa mabukata

2024-02-14 19:50:22 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun, ya yi kira da a kara samar da gudummawar jin kai a duniya, yana mai cewa kamata ya yi kasashe masu ci gaba su kara samar da gudummawar abinci, da jari cikin gaggawa ga kasashe masu tasowa dake da bukatar hakan.

Zhang Jun ya bayyana hakan ne a jiya, a gun muhawarar kwamitin sulhun MDD kan yanayi da hatsi da tsaro. Ya ce a halin yanzu, wasu kasashen Asiya da na Afirka, da Latin Amurka, suna fuskantar matsalar hatsi mai tsanani, kuma suna bukatar sassan kasa da kasa da su samar musu gudummawa.

Zhang Jun ya kara da cewa, kasar Sin ta jaddada daukar matakai bisa yanayin da ake ciki, da taimakawa kasashe masu tasowa wajen kara tinkarar sauyin yanayi, da tabbatar da samun isasshen hatsi, da magance matsalolin da yunwa da rikice-rikice suka haifar.

Jami’in ya jaddada kin amincewa da ra’ayin saka takunkumi daga bangare daya, da ra’ayin yanke hulda da hadin gwiwa da sauransu. Maimakon haka ya ce kamata ya yi a samar da yanayin duniya mai kyau ga kasashe masu tasowa, ta yadda za su iya shiga kasuwar duniya, da more alfanun sabbin sha’anoni, da kyautata tsarin raya aikin gona cikin adalci.  (Zainab Zhang)