logo

HAUSA

An yi bikin ranar rediyo ta duniya a jamhuriyyar Nijar

2024-02-14 16:27:19 CMG Hausa

Ranar jiya 13 ga watan Fabrairun shekarar 2024, kasar Nijar kamar sauran kasashen duniya, ta yi bikin ranar rediyo ta duniya, bisa taken karni guda na ba da labaru, nishadantarwa da kuma ilimantarwa.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya turo mana da wannan rahoto.

 

Ita dai wannan rana, kungiyar UNESCO ta MDD ta kirkiro ta a shekarar 2011, bisa tushen nuna muhimmiyar rawar da rediyo yake takawa a cikin zaman rayuwar dan adam tun bayan da aka kirkiro sa. A kasashen Afrika, rediyo na kasance babbar hanyar samun labarai. Shin ko rediyo yana da amfani cikin rayuwar yau da kullum? Tambayar da aza ma wasu sauraren rediyo, da ma kuma sauyin da ya kawo musu.

“Rediyo yana da amfani sosai, saboda duk abin da ba ka sani ba, kai kana zaune kana cikin duhu ne. Amma idan kana sauraren rediyo, wani abin da kake saurare sai ka ji kamar a gabanka yake. Kuma wani abin da ranka yake so ga shi nan kana ji dan jarida yana fadi. Kuma ya zo daidai da bukatunka sai ka ji dadi, ana wayar ma da mutane kai, kowa ya fahimci abin da ke tafiya. Duniyar nan fisibilillahi inda ba rediyo da yanzu muna cikin duhu.”

“Inda za ka ji labarin duniya kana nan kwance cikin daki, ka ji labarai ga su nan kala kala da wadanda ba su dadi, da wadanda suka tausayawa da kuma wadanda kake murna. Ai shi ne mahimmancin rediyo. Ni dai yanzu idan ban da rediyo ban jin dadi.”

“Gaskiya rediyo wani jigo ne na rayuwarmu, domin da shi ne muke sanin yaya duniya take ciki, gaskiya rediyo na da matukar mahimmanci sosai.”

“Sauraren rediyo yana kawowa mutum wayewar kai, yana kawowa mutum sanin abin da ba ka sani ba, kuma har yanzu wani abu ko da yana faruwa, kai kana zaune ba ka san da shi ba, amma idan kana sauraren rediyo kana iyar ka san wannan abun yana faruwa.”

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.