logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su samar da yanayi mai kyau na warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa

2024-02-13 16:20:35 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana a gun taron kwamitin sulhun MDD kan batun Ukraine a jiya cewa, ya kamata kasa da kasa su kara himma wajen samar da zaman lafiya, da tattaunawa don samar da yanayi mai kyau wajen sassanta rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. Ya kamata wasu kasashe su daina tada rikici su daina zagon kasa ga kokarin diflomasiyya na kasashen duniya.

Zhang Jun ya ce, a ko da yaushe Sin tana ci gaba da kiyaye batun Ukraine cewa, ya kamata a mutunta 'yancin kai da cikakken yankin dukkan kasashen duniya, da kiyaye manufofi da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD, da daukar kwararan matakan tsaro na dukkan kasashe da muhimmanci, kana ya kamata a goyi bayan duk wani kokari da zai taimaka wajen warware rikicin cikin lumana.

Zhang Jun ya ce, kasar Sin ce mai kiyaye tabbatar da zaman lafiya a duniya, da tabbatar da zaman lafiya da adalci. Sin tana son yin aiki tare da kasa da kasa don sa kaimi ga warware rikicin Ukraine da sauran batutuwa ta hanyar siyasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya. (Zainab)