logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya ce yana goyon bayan duk wani shiri da zai kawo sauki ga alhazan kasar a bana

2024-02-13 16:26:07 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada mahimmancin addu’o’i wajen ginuwar kasa, inda ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa wajen tallafawa dukkan wasu hidin-dimu da suka shafi addinai.

Ya tabbatar da hakan ne a fadarsa dake birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin tawagar kungiyar Tijjaniyya na duniya karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Mahe Niass, ya ce malaman addinai na bayar da gagarumar gudummowa wajen samun nasara gwamnatin sa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su koma ga Allah ta hanyar rike amanar juna da kishin kasa da kuma dauke kai daga duk wani abu da yake da nasaba da cin hanci ko rashawa.

Ya shaidawa bakin nasa cewa gwamnati na bakin kokarin cimma burinta na wadata kasa da abinci ta hanyar kawo sauye-sauye a harkar noma domin ganin Najeriya ta kasance mai dogaro da kanta wajen samar da abinci da kuma fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen waje. Ya ce a halin yanzu ma gwamnati ta yi odar dubban motocin noma domin samun damar noman amfani mai yawan gaske.

“Aikin da muke yi a halin yanzu ya yi daidai da koyarwa da muka samu daga manzon Allah, Annabi Muhammadu S-A-W, lura da jin dadin rayuwar al’umma, wanda ta sa za mu samarwa dukkannin asibitoci kayayyakin aiki na zamani, bayar da horo ga likitoci, ta yadda za su kula sosai ga marasa lafiya, haka kuma za mu tabbatar da ganin shirinmu na inshorar lafiya ya kai ga kan kowanne dan kasa.”

A kan batun aikin hajji kuwa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamantinsa a shirye take wajen goyon bayan duk wani tsari da aka tabbatar zai kawo sauki ga alhazan kasar a yayin aikin hajjin bana.

Da yake jawabinsa jagoran tawagar kungiyar ta Tijjaniyya na duniya Sheik Mahe Niass yabawa shugaban kasar ya yi bisa kokarin da yake yi a ko da yaushe wajen tabbatar da tsaro da hadin kan kasa.(Garba Abdullahi Bagwai)