logo

HAUSA

Manyan jami’an kasashe mambobin kungiyar kasashen yankin Sahel AES na taro a birnin Ouagadougou

2024-02-13 16:24:41 CMG Hausa

An bude taron manyan jami’an kasashe mambobin kungiyar kasashen yankin Sahel AES a jiya Litinin 12 ga watan Fabrairun shekarar 2024 a birnin Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Wannan taro da ke gudana kwanaki kalilan bayan matakin ficewa ba tare da wani jinkiri ba na kasashe uku na AES daga kungiyar CEDEAO ko ECOWAS na da manufar gaggauta tsarin dunkulewa na kasashen Liptako-gourma domin kai ga moriyar cimma kafa wata gamayya tsakanin Burkina Faso, Mali da kuma Nijar.

A lokacin bude taron, a cikin jawabin sakatare janar na ma’aikatar harkokin wajen kasar Burkina Faso, ya bayyana cewa wannan taro da kasarsa take karba yana da muhimmancin gaske ga makomar wadannan kasashe. Amma kafin sannan saida kuma shugabannin tawagogin Mali da Nijar suka yi nasu jawabi, inda na kasar Nijar jakada Ousmane Alhassane, mai bada shawara a ma’aikatar harkokin wajen kasar Nijar da hulda da ‘yan Nijar da ke ketare, ya bayyana cewa, nauyi ya rataya gare su na aza tubalin makomar wadannan kasashe, domin ci gaban al'ummarsu da ci gaban kasashen nasu baki daya.(Mamane Ada)