logo

HAUSA

AFCON 2023: Cote d'Ivoire ta lashe kofin kwallon kafan Afirka

2024-02-12 15:35:27 CMG Hausa

 

A jiya ne, kasar Cote d'Ivoire mai masaukin bakin gasar wasan kwallon kafan nahiyar Afirka (AFCON), ta lashe gasar karo na 34 da aka buga a birnin Abidjan, inda ta doke kasar Najeriya a wasan karshe da ci biyu da daya.

Duk da yadda ‘yan wasan Cote d'Ivoire suka mamaye wasan da kashi 65 cikin 100, Najeriya ce ta fara cin kwallo a mintuna na 38 da fara wasa, ta hannun kyaftin din ta William Troost-Ekong wanda ya ci kwallon da kai bayan bugun kusurwa.

Sai dai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, a minti na 62 Cote d'Ivoire ta rama cin da aka yi mata ta hannun Franck Kessié bisa taimakon Simon Adingra.

Cote d'Ivoire ta ci kwallo na biyu ne ta hannun dan wasan gaba Sébastien Haller, a minti na 81.

Wannan shi ne karo na uku da tawagar Cote d'Ivoire ke lashe gasar cin kofin kwallon kafan nahiyar Afirka, bayan wanda ta lashe a shekarar 1992 da ta 2015. (Ibrahim)