logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai Rafah ya zarce 100

2024-02-12 15:48:13 CMG Hausa

 

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu (WAFA) ya ruwaito cewa, yawan mutanen da suka mutu a munanan hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a birnin Rafah a kudancin zirin Gaza da yankunan da ke kusa da birnin, ya zarce 100 tare da jikkata wasu daruruwan da suka hada da mata da kananan yara.

Sanarwar ta bayyana cewa, kimanin hare-hare ta sama 40 ne sojojin Isra’ila suka kai a yankin Rafah da sanyin safiyar Litinin din nan, baya ga luguden wuta ta kasa.

Wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar na cewa, ta kai jerin hare-hare kan wuraren 'yan ta'adda a kudancin Gaza a yau, amma ba ta yi wani karin bayani ba.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a jiya Lahadi cewa, adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a zirin Gaza, ya karu zuwa 28,176 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa yanzu, yayin da wasu 67,784 suka jikkata.

Tun bayan barkewar rikicin Isra'ila da Hamas a Gaza, kusan rabin mazauna wurin ne suka tsere zuwa Rafah da ke kusa da kasar Masar, domin neman tsira.

Garin da ke kan iyaka da ke samun tallafin abinci da magunguna daga kasashen waje da kuma hukumomin MDD ta mashigar Rafah, cike yake da tantuna da aka kafa a filayen noma da babu kowa, da makarantu da kuma gefen tituna.(Ibrahim)