logo

HAUSA

Hukumomin Nijar: An gano wata ma’ajiyar kayayyakin soja a tsakiya maso gabashin Nijar don kawo tashin hankalin cikin kasa

2024-02-12 16:06:29 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, sojojin kasar ne suka ba da wani labarin gano wata ma’ajiyar makamai da kayayyakin soja a yankin Zinder. A cewar hukumomin kasar, wadannan kayayyaki an shigo da su domin kawo tashin hankali cikin kasar Nijar tare da hannun tsoffin shugabannin kasa.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto.

 

A wani labari da gidan talabijin na kasa RTN ko Télé Sahel na ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairun shekarar 2024, da ya ambato mujallar rundunar sojojin Nijar FAN na cewa, jami’an tsaro na FDS na Nijar da ke bangaren tsaro na shiyya ta 3 dake yankin Zinder sun sanar da cewa sun gano wani wurin da aka boye tarin makamai da kayayyakin soja a kauyen Tesker da ke cikin yankin Zinder da ke tsakiya maso gabashin kasar Nijar. A cewar wannan mujallar, wadannan makamai da kayayyakin soja na mallakar wasu mutane na kusa da tsohon shugaban kasa, Mohamed Bazoum. Mujallar ta FAN ta kara da cew, wadannan kayayyaki da aka gano sun hada da nakiyoyi 20 da ke tarwatsa tankokin yaki tare da tsarin tada su daga nesa, domin kawo tashin hankali a cikin birane, da kuma wata na’urar kakkabo jiragen yaki, in ji mujallar rundunar sojojin Nijar ta FAN.

Tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP sun bayyana cewa, kasar na cikin barazana ta abokan gaba daga ko’ina.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.