logo

HAUSA

Sin tana bunkasa aikin gona tare da kyautata muhallin halittu

2024-02-12 16:01:13 CMG Hausa

Ma’aikatar aikin gona da raya kauyuka ta kasar Sin ta bayyana cewa, Sin ta bunkasa aikin gona da kyautata muhallin halittu a shekarar 2023.

Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, an samu ci gaba a fannin samar da kayayyakin noma masu inganci a shekarar 2023, yawan sabbin kayayyakin noma da aka yi rajista saboda ingancinsu da samar da su ba tare da gurbata muhalli ba, ya kai dubu 15. A sa'i daya kuma, dokar hana kamun kifi na tsawon shekaru 10 a kogin Yangtze, ta cimma muhimman sakamako masu muhimmanci, an kuma tabbatar da zaman rayuwar masu kamun kifi a yankin fiye da dubu 230, da albarkatun halittu na ruwa da kogin yana farfadowa.

Bayanai na cewa, kasar Sin za ta kara bunkasa sha’anin noma da kyautata muhallin halittu tare, da raya fannonin musamman na kauyuka, da sa kaimi ga hada sha’anin noma da masana’antu da samar da hidimomi tare a kauyuka, da kuma karfafa gina ababen more rayuwa, masana'antu da yankunan karkara masu kyan gani. (Zainab Zhang)