logo

HAUSA

Masana’antar Samar Da Kayayyaki Ta Kasar Sin Ta Samu Farfadowa A Shekarar 2023

2024-02-11 16:28:35 CMG Hausa

Alkaluma sun nuna cewa, masana’antar samar da kayayyaki ta kasar Sin, ta ci gaba da farfadowa a shekarar 2023, haka kuma kudin shigar da ta samu ya karu cikin watanni 5 a jere.

A cewar hukumar bayar da kididdiga ta kasar Sin (NBS), a bara, kudin shigar da manyan kamfanonin masana’antar suka samu, wadanda kudin shigarsu a shekara ya kai a kallakudin Sin RMB yuan miliyan 20 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 2.82, ya karu da kaso 1.1 a kan na shekara 1 da ta gabace ta.

A rubu’i na 4 na shekarar 2023 kuma, kudin shigar wadannan kamfanoni ya karu da kaso 3.2, yayin da saurin ci gaban da suka samu ya karu da maki kaso 2.9 fiye da na rubu’i na 3.

A cewar Yu Weining, jami’in hukumar NBS, ayyuka a masana’antar sun ci gaba da fadada cikin juriya, lamarin da ya samar da kyakkyawan yanayin ci gaba da farfadowar ribarsu.

Ya kara da cewa, a mataki na gaba, kasar Sin za ta fadada bukatu na cikin gida, da karawa harkokin kasuwanci daban daban kuzari da inganta dogaro da kai a bangaren ingantattun kimiyya da fasaha da gaggauta bunkasa tsarin ayyukan masana’antu na zamani, a matsayin wani yunkuri na inganta ci gaba mai inganci ga tattalin arzikin masana’antu. (Fa’iza Mustapha)