Ministocin kudi na kasashen yammaci da tsakiyar Afrika sun bukaci karin rangwame daga bashin bankin duniya
2024-02-11 16:02:18 CMG Hausa
Ministan kudi da bunkasa tattalin arzikin Najeriya Mr. Wale Edun ya kawo shawarar karin samun rangwame daga irin basussukan da bankin duniya ke baiwa kasashen yammaci da tsakiyar Afrika domin su samu sukunin shawo kan kalubalen dake gaban su.
Ya bukai hakan ne a madadin takwarorinsa, yayin taron tattaunawa a kan sauye-sauyen tattalin arzikin kasashen Afrika wanda ministocin kasashen yammaci da tsakiyar nahiyar da kuma wakilan bankin duniya suka gudanar a birnin Abuja.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan kudin na Najeriya ya kawo shawarar ce a daidai lokacin da bankin na duniya ya sanar da bayar da dala biliyan 44 ga kasashen Afrika, inda ya ce adadin kudaden da bankin ke tunkudowa kasashen Afrika ya tashi daga dala biliyan 2 a shekara ta 2000 zuwa biliyan 10 a 2020 sai kuma biliyan 28 a halin yanzu.
Mr. Wale Edun ya kara da cewa, duk da dai cibiyar nan ta Bretton Woods na bayar da gagarumin tallafi ga nahiyar ta Afrika ta fuskar kudade da sauran al’amura, amma dai har yanzu kasashen na bukatar karin tallafi.
“Mun kasance a nan ne domin mu tattauna a kan cigaba da samun kudade da samar da makamashin wutar lantarki da ma sauran mahimman batutuwan da suka shafi matalautan kasashe kana da irin rawar da bankin na duniya ya kamata ya taka a matsayinsa na abokin kawo cigaba.”
Ministan ya bayyana cewa, daukacin takwarorinsa da suka halarci taron sun matsa kaimi sosai kan bukatar samun rangwame wajen kudaden da bankin na duniya ke bin kasashensu.
A jawabinta manajan daraktan sashen gudanarwar ayyukan na bankin duniya Miss Anna Bjerde jaddada kudirin bankin ta yi wajen ci gaba da samar da kudade ta fuskoki daban daban domin kare afkuwar tashe- tashen hankula da kuma tallafawa hadin kan nahiyar baki daya.
“Rawar da bankin duniya ke takawa yana da mahimmanci a yanzu fiye da na ko yaushe, za mu ci gaba da aiki da ku kafada da kafada domin kaiwa ga samun kyakkyawar makoma da wadata ga kasashenku.” (Garba Abdullahi Bagwai)