logo

HAUSA

Shugaba Xi Da Uwargidansa Sun Aike Da Gaisuwar Sabuwar Shekarar Gargajiya Ga Malamai Da Daliban Makarantar Lincoln Ta Amurka

2024-02-11 16:17:22 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun amsa sakon gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da malamai da daliban makarantar sakandare ta Lincoln ta kasar Amurka suka aika musu, inda suka yi musu fatan alheri a shekarar Loong.

Cikin nasu sakon gaisuwar ga malamai da daliban, Xi da Peng sun gayyace su da su ziyarci kasar Sin a kai a kai, har ma da shiga shirye-shiryen karatu na musaya dake gayyatar matasan Amurka 50,000 zuwa Sin, da nufin bayar da gudummowarsu ga inganta abota tsakanin al’ummomin biyu, musamman tsakanin matasa.

Da farko, malamai da daliban sun aike da katin gaisuwar sabuwar shekara tun daga birnin Washington na Amurka, zuwa ga Xi da Peng da al’ummar Sinawa, inda suka yi musu fatan alheri da farin ciki da koshin lafiya a sabuwar shekara. Malamai da dalibai sama da 100 ne suka rattaba hannu kan katin gaisuwar. (Fa’iza Mustapha)