logo

HAUSA

‘Yan kasar Sin mazauna birnin Kano dake arewacin Najeriya sun gudanar da liyafar murna sabuwar shekara Sinawa

2024-02-10 15:55:32 CMG Hausa

A jiya juma’a 9 ga wata, ‘yan kasuwar kasar Sin dake zaune a birnin Kano da ke arewacin Najeriya suka gudanar da liyafar cin abincin dare domin murnar sabuwar shekarar Sinawa ta 2024 da ta fara daga yau din nan Asabar.

An dai gudanar da liyafar ce a katafaren gidan abinci na Red China restaurant dake unguwar Nasarawa GRA a birnin Kano, inda dukkannin wadanda suka halarci liyafar suka yi fatan samun karuwar arziki da zaman lafiya a duniya baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya halarci wajen liyafar, ga kuma rahoton da ya aiko mana.

 

Kamar dai kowacce shekara, ‘yan kasuwar ta kasar Sin tare da iyalan su dake gudanar da harkokin kasuwanci a jihar Kano su kan taru a wannan gidan abinci domin taya juna murnar shigowar sabuwar shekarar Sinawa.

Cikin farin ciki da nishadi, sun bayyana gamsuwa bisa karamcin da suka samu daga ‘yan Najeriya a shekarar da ta gabata, inda suka yi fatan samun ninkin hakan a wannan sabuwar shekarar.

Sun yi bayanin cewa zaman lafiya shi ne babban sinadarin da zai kara karfafa musu gwiwa wajen ci gaba da saka jarinsu a Najeriya, inda suka yaba da kokarin gwamnatin kasar wajen tabbatar da dauwamammen zaman lafiya a dukkan sasan kasar.

Haka kuma sun yi fatan ci gaba da samun karuwar harkokin tattalin arziki a Najeriya da kuma kasar China.

“Ina murna da sabuwar shekarar Sinawa, komai yana tafiya daidai kuma cikin farin ciki, kuma ina fatan kowa ya zama mai arziki a 2024”, “Daga nan Najeriya muke murna sabuwar shekarar kasar Sin, farin cikin mu ba zai taba misaltuwa ba”, “ Suna na Mr Liu, barka da sabuwar shekara, ina taya kowa da kowa murna tare da fatan samun karuwar kudade a cikin wannan shekara”.(Garba Abdullahi Bagwai)