Sojojin Nijar sun dakile wani gungun mutane dauke da makamai a arewa maso gabashin birnin Arlit
2024-02-10 16:12:42 CMG Hausa
A jamhuriyar Nijar, an yi bata kashi tsakanin jami’an tsaro na FDS da mutane dauke da makamai, a yayin da sojojin suke bada kariya kan ayarin masu neman zinari bisa hanyarsu ta dawowa Arlit.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A yayin wani taron manema labarai a ranar jiya 9 ga watan Fabrairun shekarar 2024, kwamandan Almoustapha Ousmane, ferfen Arlit ya yi karin haske inda ya bayyana cewa sojojin Nijar sun samu murkushe wadannan miyagun mutane ta hanyar lalata motoci 2 da kashe wasu daga cikinsu da kama makamai da dama da kuma alburusai.
Ferfen ya kara da cewa, “A ranar Laraba da ta wuce, 7 ga watan Fabrairun shekarar 2024, ayarin jami’an tsaro na FDS da ke ba da kariya ta fada cikin wani kwaton bauna na masu mugun niyya nan arewa maso gabashin birnin Arlit, wajen kilomita 300 da wani abu. Mun gode ma Allah da yake sojajawa sun sanu horo tun da su masu mugun miyya sun saci abubuwa da yawa kamarsu motoci da bindigogi. Muna kai namu gaisuwa, da na shugaban kasa Tiani Abdourahamane da na firaminista bisa ga wannan kuma al’umma na Arlit kun ga fitowar da al’ummar Arilit, sun babbar, sai da Allah. Ina kai musu godiya, Allah ya saka musu da suka zo tare da himma. Mun godewa Allah, mun godewa sojojinmu.”
Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.